Wani jigon dan Majalisar Dokokin Amurka ya gargadi shugaba Barack Obama cewa zai sabawa doka muddin Amurka ba ta tsame hannunta a fafatawar da ake yi a Libiya ba daga ran Lahadi mai zuwa, ko kuma ya nemi amincewar Majalisa na ci gaba da fafatawar kuma ya sami amincewarta.
Kakakin Majalisar Wakilai, dan Republican John Boehner, ya yi gargadin ne a jiya Talata cikin wata wasikar da ya aike wa Obama.
Boehner ya nemi da shugaba Obama ya yi bayani zuwa Jumma’a game da hurumin da aka dogara a kai wajen fafatawa a Libiya.
A martaninsa ga wasikar ta Boehner, kakakin Fadar White House Tommy Vietor y ace aka mataki na karshe na harhada bayanai ga Majalisar game da abubuwa da daman a fafatawar Amurka a Libiya. Ya ce gwamnatin Obama za ta kuma yi bayanin huruminta a karkashin Dokar Halatta Yaki ta 1973.
A watan Maris Mr. Obama ya sanar da Majalisar Dokokin Amurka niyyarsa ta daukar matakin soji a Libiya, ba tare da ya nemi amincewar Majalisar ba.