Ma'aikatan Kiwon Lafiya a Adamawa Sun Tada Jijiyar Wuya Akan Albashinsu

Ma’aikatan kiwon lafiya dari takwas da talatin da uku da suka share shekara daya da wata biyar babu albashi sun shiga kwana na biyu suna zaman durshan a jihar Adamawa.

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da hukumar kula da jin dadin ma’aikatan kiwon lafiya da ke Yola fadar jihar Adamawa ke gudanar da aikin tantance ma'aikata karo na uku.

Makasudin wanna aikin na tantancewa shine don gano ma'akatan ainihi don a biya su albashinsu. Amma wasu na ganin babu adalci a aikin tantancewar da ake yi.

Ma'aikatan dai sun koka akan cewa sun galabaita, sun kuma zargi daraktocin hukumar da sayar da takardar shaidar daukar aiki kan naira dubu hamsin zuwa dubu dari, yayin da wadanda su ke halartattu kuma ake maye gurbin sunayen su da sabbi, dalilin da ya sa suka tarwatsa zaman kwamitin da ke aikin tantancewar.

Kwamishiniyar ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Adamawa Dr, Fadimatu Atiku Abubakar wadda ta tabbatar da afkuwar lamarin, ta bi ba'asin zargin cin hanci da aka yi amma ta ce ma'aikatan sun musanta zancen.

Ma’aikatan na daga cikin rukunin ma’aikata da zasu anfana daga tallafin gwamnatin tarayya na naira biliyan tara da gwamnatin jihar ta karba domin biyan ma’aikata hakkokinsu.

Ga karin bayani daga Sanusi Adamu.

Your browser doesn’t support HTML5

Ma'aikatan kiwon lafiya a Adamawa sun tada jijiyar wuya akan albashinsu - 3'10"