A jihar Bauchi nakasassu sun taru a wannan ranar domin su jawo hankalin jama'a da gwamnati akan irin halin da suke ciki.
Malam Haruna Saidu Pali shugaban kungiyar nakasassu ta jihohin arewa maso gabas ya mika sako ga al'umma akan kyamar da ake yiwa nakasassu. Yace suna yaki da irin wannan halin. A bangaren gwamnati yace kamar yadda lafiyayyu ke kukan rashin aikin yi haka su ma su keyi. Yace bara da su keyi ta zama masu dole ne. Muddin ya samu abun yi shi da bara saidai tarihi.
Shugaban matasan nakasassu na jihar Bauchi ya godewa Allah da zagayowar ranar. Suna fuskantar kalubale da dama.Akwai mutanensu da dama da suka yi karatu amma sai su dawo su zauna babu abun yi. Wadanda kuma suka koyi sana'o'i basu da jarin da zasu yi kasuwanci.
Wani Abubakar Abdullahi shi nakasashe yace yana cikin wadanda suke fama da ciwon wanda ya hanasu gani sosai. Ya kira gwamnati ta zo ta airin abubuwanaikin hannu da su keyi.
Ita ma Amina Idris tace babu abun da ya kai bara wulakanci saboda haka suna bukatar tallafi idan har an daukesu mutane.
Ga karin bayani.