Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Al'ummar Igbo Mazauna Neja Sun Nesanta Kansu daga Masu Neman Kafa Biafra


Nasu zanga zangar neman kafa kasar Biafra
Nasu zanga zangar neman kafa kasar Biafra

Yayinda lamura ke zafafa a yankin kudu maso gabashin Najeriya akan neman kafa kasar Biafra daga Najeriya 'yan asalin yankin dake jihar Neja sun ce ba dasu a keyi ba

Al'ummar Igbo din dake jihar Neja sun kira taron manema labarai inda shugabansu a jihar Chief Ezegbu Emmanuel ya bayyana cewa matsayinsa akan lamarin shi ne kira ga gwamnatin Najeriya da ta hau teburin tattaunawa maimakon yin anfani da karfi.

Akan fafutikar da wasunsu keyi na ganin an kirkiro Biafra daga tarayyar Najeriya Chief Emmanuel yace babu mutumin Igbo da ya san abun da ya faru lokacin yakin basasa da zai yi mafarkin sake shiga irin wannan yakin ba.

Ita gwamnatin jihar Nejan ta yi maraba da matakin da al'ummar Igbon suka dauka. Jibril Baba Ndace kakakin gwamnan jihar Neja yace gwamnan yana goyon bayan mutanen Igbo dake zaune a jihar.

Ranar 12 ga wannan watan 'yan kabilar Igbo din dake Neja zasu gudanar da wani gangami da suka sanya ma suna "macin zaman lafiya" a garin Suleja.

A nasu bangaren majalisar limaman jihar Neja sun ce sun dukufa wajen bayyanawa al'umma mahimmancin furta kalamun hada kan jama'a a daidai wannan lokacin.

Sakataren majalisar limaman Imam Faruk Abdullahi yace basu ji dadin kalamun shugaban kungiyar Kiristocin Arewa ba Bishop Matthew Hassan Kukah.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG