Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yobe: Kotun Daukaka Karar Zabe Ta Mayarwa Dan Dan Takar PDP Kujerarsa


Mai shari'a cikin kotu
Mai shari'a cikin kotu

A shari'ar farko da kotun sauraran kararrakin zabe ta yanke ta soke zaben Alhaji Sabo Garba na jamm'iyyar PDP dake wakiltar mazabar Nange da Potiskum a jihar Yobe ta ba dan takarar APC amma yanzu kotun daukaka kara ta mayar masa da kujerar

Alhaji Sabo Garba tun da farko ya lashe zaben majalisar wakilai ta tarayya daga mazabar Nange da Potiskum dake jihar Yobe a tutar jam'iyyar PDP.

Saidai kotun saurara kararrakin zabe ta soke zaben nashi bisa zargin da ya jibanci takardar shaidar makarantar firamare. Kotun ta bada umurnin a rantsar da Ali Yakubu Mainasara na jam'iyyar APC.

Biyo bayan daukaka kara da Sabo Garba ya yi kotun daukaka kara da ta zauna a Abuja ta yi watsi da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe ta kuma bukaci Sabo Garba da ya cigaba da zama wakili a majalisar tarayya.

Shi Sabo Garba ya yiwa Allah godiya da ya tabbatar da zabensa. Yace gaskiya gaskiya ce kuma karya karya ce. Yanzu kotun daukaka kara ta tabbatar da gaskiyar.

Malam Abdulwasiu Potiskum na bangaren Ali Yakubu Mainasara na jam'iyyar APC yace shari'a bata yi masu dadi ba. Yace komi na Allah ne amma su magoya bayansa sun yadda da hukuncin kotun daukaka kara.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:35 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG