Da yake karanta hukuncin kotun a madadin alkalan kotun biyu, mai shara’a Ridwan Maiwada Abdullahi ya yi watsi da umurnin da kotun ta jihar Taraba ta bayar na a sake gudanar da zabe a wasu mazabu.
Tun da farko dan takarar kujerar majalisar dattawa na Taraba ta arewa, Mal. Ali Sani Kona na jam’iyar APC, ya shigar da kara yana kalubalantar zaben Sanata Sani Abubakar Danladi na jam’iyar PDP da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa .
Wakilin Sashen Hausa, Sanusi Adamu ya halarci zaman kotun. Ya kuma shaida cewa kotun ta tabbatarwa Sanata Sani Abubakar Danladi da kujerarsa.
Ya zuwa yanzu dai, kotun daukaka kararrakin zaben ta yanke hukunci akan korafe-korafe guda 2 kenan a jihar Taraba, da farko ta kwace kujerar majalisar dattawa ta Taraba ta tsakiya daga hannun sanata Bashir Marafa na jam'iyyar PDP ta ba sanata Yusuf A Yusf na jam'iyyar APC da kuma tabbatar da kujerar.
Ga karin bayani cikin sauti.