Lauyan Nnamdi Kanu Ya Ce Kenya Ta Azabtar Da Kanu Yayin Da Ya Ke Hanunsu

Nnamdi Kanu, Jagoran Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra, IPOB

Lauyan shugaban kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Efeanyi Ejiofor, ya ce an azabtar da wanda ya ke karewa, Nnamdi Kanu yayin da ya ke a tsare a hannun hukumomin Kenya.

Efeanyi Ejiofor yace yana da kwararun shaidu da zai gabatar wa Kotun Shari'a ta Duniya game da take hakkin Nnamdi Kanu.

Duk yunkurin Muryar Amurka to samo martani nan take daga gwamnatin Kenya ya ci tura.

A farkon makon nan ne, Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba wa jami'an tsaron Najeriya saboda rawar da suka taka wajen aiwatar da aiki na kasa da kasa da ya yi sanidiyar kama Kanu.

Duk da haka, Shugaba Buhari bai bayar da bayanai kan aikin ba sai dai kawai an tsare Kanu ne saboda hadin gwiwar kasa da kasa.

Karin bayani akan: Nnamdi Kanu, Igbo, Biafra, Biyafara, DSS, IPOB, Abuja, Nigeria, da Najeriya.

Kungiyar Kanu tanafafutikar kafa kasa mai cin gashin kanta ta kabilun Ibo a kudu maso gabashin Najeriya. Gwantin Najeriya ta dauki kungiyar a matsayin kungiyar ta'adda.

Lauya Ejiofor ya ce wannan lakabin na 'yan ta'adda yaudara ce ga gwamnatin Najeriya don kame mambobin kungiyar IPOB.

Ejiofor ya fadawa wakilin Muryar Amurka James Butty cewa yayin da kasashen duniya suka kasafta kungiyoyi kamar su Fulani Makiyaya da Boko Haram a matsayin kungiyoyin 'yan ta'adda, ba haka IPOB ya ke ba.

Ana sa ran kotun zata cigaba ranar 26 ga watan Yuli, kuma Ejiofor ya ce yana da kyakkyawan fata Kanu zai yi nasara a kotun shari'a.