Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Ba Da Umarnin A Tsare Nnamdi Kanu A Ofishin DSS


Nnamdi Kanu (Hoto: AP)
Nnamdi Kanu (Hoto: AP)

Kanu zai sake bayyana a gaban kotun a ranar 26 ga watan Yuli don ci a gaba da sauraren shari'ar.

Babbar kotun tarayya da ke Abuja, ta ba da umarnin a tsare shugaban kungiyar IPOB Nnamdi Kanu a ofishin hukumar tsaro ta DSS da ke birnin na Abuja.

An sake gurfanar da Kanu ne bayan da aka kamo shi daga kasar waje kamar yadda babban Atoni-Janar din kasar Abubakar Malami ya fada a wani taron manema labarai a ranar Litinin.

Rahotanni sun ce Mai Shari’a Binta Nyako ta amince da matso da shari’ar ta Kanu daga 20 ga watan Oktoba zuwa 26 da 27 ga watan Yuli.

Hakan na nufin zai sake bayyana a gaban kotun a ranar 26 ga watan Yuli.

Nnamdi Kanu bayan da aka kamo shi daga kasar waje (Hoto: Fadar Gwamnatin Najeriya)
Nnamdi Kanu bayan da aka kamo shi daga kasar waje (Hoto: Fadar Gwamnatin Najeriya)

Karin bayani akan: Nnamdi Kanu, Biafra, DSS, IPOB, Binta Nyako, Ministan Shari’a Abubakar Malami, Nigeria, da Najeriya.

Yayin zaman shari'ar, jaridar Tribute ta ruwaito cewa Nnamdi Kanu ya fadawa kotun cewa ya gudu a kasar ne saboda an yi yunkurin a halaka shi.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, bayan kammala zaman shari’ar, jami’an DSS sun sulale da shi ta hanyar da alkali ke bi wajen shiga kotun suka fice da shi.

A watan Oktobar shekarar 2015 aka kama Nnamdi Kanu bisa laifuka 11 da ake tuhumar shi akai, wadanda suka hada da cin amanar kasar, jagorantar kungiyar da ke ta da zaune tsaye da kuma mallakar makamai.

An ba da belinsa a watan Afrilun 2017 bisa dalilai da suka shafi rashin lafiya, amma ya tsere daga Najeriyar bayan wani samame da dakarun kasar suka kai gidansa da ke Umuahia a jihar Abia.

Ana zargin kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra da kai hare-hare akan jami’an tsaro da gine-ginen gwamnati, zargin da suka sha musantawa.

A shekarar 2017 hukumomin Najeriyar suka haramta kungiyar tare da saka ta cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda.

Sake kama Kanu na zuwa ne kasa da mako biyu bayan da gwamnoni da shugabannin yankin kudu maso gabashin Najeriya suka nesanta kansu da ayyukan kungiyar musamman kan batun fafutukar ballewa daga Najeriya.

Saurari hirar Ministan Shari’a Abubakar Malami da wakilinmu Umar Faruk Musa:

Kotu Ta Ba Da Umarnin A Tsare Nnamdi Kanu A OfIshin DSS - 2'16"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00

Nnamdi Kanu: ​An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi

Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:05 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG