A cikin wani shirin siyasa na gidan rediyon Najeriya, Ministan watsa labarai Lai Mohamed ya ce an dakatar da Twitter a Najeriya ne saboda zargin ana amfani da kafar wajen yayata manufofin wasu da ke da kudurin wargaza kasar, ba wai don ta shafe jawabin shugaba Muhammadu Buhari ba, kamar yadda wasu ke zargi.
“Twitter ta kasance babban zabi ga wani da ke hankoron raba kan kasa,” a cewa Lai Mohamed.
Ya ci gaba da cewa “dan awaren ya dage da amfani da kafar Twitter wajen baiwa mabiyansa umarnin su kashe sojoji da ‘yan sandan Najeriya, tarwatsa ofisoshin hukumar zabe da lalata duk wata alama ta kasancewar Najeriya ‘yantacciyar kasa.”
To sai dai minstan ya ce ko kadan kamfanin na twitter bai taba daukar yunkurin da jagoran ‘yan awaren yake yi da muhimmanci ba.
Ya ce sam ba wani hakuri da gwamnatin Najeriya za ta ba wadanda ba su ji dadin dakatar da twitter da aka yi a kasar ba, domin kuwa a cewar sa, wajibi ne kasa ta sami zama lafiya, kafin ‘yan kasar su morewa ‘yancin fadar albarkacin baki.
Karin bayani akan: PDP, Twitter, Jack Dorsey, Shugaba Muhammadu Buhari, Lai Mohamed, Nigeria, da Najeriya.
Lai Mohamed ya ci gaba tare da dora alhakin dukan tashe-tashen hankula da koke-konen da aka yi a lokacin zanga-zangar kin jinin SARS, akan twitter da shugaban ta Jack Dorsey.
Ya yi zargin cewa Jack Dorsey ya tara kudade ta hanyar ‘bitcoins’ wadanda yayi amfani da su wajen daukar nauyin zanga-zangar ta nuna kin jinin SARS, yayin da kuma aka yi amfani da kafar sa ta twitter wajen ruruta rikicin.
Ministan ya kafa hujja da wata jaridar yanar gizo da bai ambaci sunan ta ba, da ya ce a binciken da ta yi na bin kwa-kwaf, ta dorawa Jack Dorsey laifi, akan rawar da ya taka wajen ruruta zanga-zangar.
Ya ce jaridar ta tabbatar da Jack Dorsey ya maimaita wasu sakwannin jagororin zanga-zangar, haka kuma ta tabbatar da cewa Jack Dorsey ya kaddamar da asusun tarbacen kudi ta hanyar bitcoins, domin tallafawa masu zanga-zangar.
Wannan a cewar Ministan, ya yi sanadiyyar kona motoci 64 da ofisoshi 134 na ‘yan sanda, tare da fasawa da wawushe kamfanonin masu zaman kan su har 265 a fadin kasar.
Gwamnatin Najeriya dai ta dakatar da amfani da kafar sadarwa ta Twitter a cikin kasar, sa’o’i 24 bayan da kamfanin ya goge jawabin shugaban kasar Muhammadu Buhari kan sha’anin tsaron kasa.
Wannan matakin dai ya bakantawa wasu da ciki da wajen Najeriya rai, ciki har da wasu kasashe irin Amurka, har suka fito fili suka soki lamirin matakin na gwamnati.
To sai dai a makon jiya Ministan watsa labarai Lai Mohamed ya bayyana cewa an soma tattaunawa domin sasantawa da kamfanin.
Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi