Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Shugaban Kungiyar IPOB Nnamdi Kanu


Nnamdi Kanu, Jagoran Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra.
Nnamdi Kanu, Jagoran Kungiyar Fafutukar Kafa Kasar Biafra.

A cewar Malami, an yi nasarar cafke shi ne tare da hadin gwiwar rundunar ‘yan sandan kasa da kasa ta Interpol.

Rahotanni daga Najeriya na cewa an kama jagoran kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra, Nnamdi Kanu.

Babban Atoni-Janar din kasar kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja a ranar Talata.

Bayanai sun yi nuni da cewa an kama shi ne a kasar waje.

A cewar Malami, an yi nasarar cafke shi ne tare da hadin gwiwar jami'an tsaron Najeriya.

Karin bayani akan: Nnamdi Kanu, Biafra, IPOB, Ministan Shari’a Abubakar Malami, Nigeria, da Najeriya.

Nnamdi Kanu bayan da aka kamo shi daga kasar waje (Hoto: Fadar Gwamnatin Najeriya)
Nnamdi Kanu bayan da aka kamo shi daga kasar waje (Hoto: Fadar Gwamnatin Najeriya)

A shekarar 2017 Kanu ya tsere daga Najeriya bayan da wata babbar kotun tarayya ta ba da belinsa bisa dalilai na rashin lafiya.

An gindaya masa wasu sharudda da suka hada da kaucewa yin hira da manema labarai, sharadin da ake zargin ya take.

A shekarar 2019 kotu ta soke belin da ta ba shi.

Gabanin ya fice daga kasar, dakarun Najeriya sun kai wani samame gidansa da ke Afara-Ukwu da ke kusa da garin Umuahia a jihar Abia, inda tun daga lokacin ba a kara jin duriyarsa ba sai a kasar waje.

Ana tuhumar Kanu ne da laifuka 11 da suka shafi cin amanar kasa da jagorantar kungiyar IPOB da ke ta da zaune tsaye hade da mallakar makamai.

A shekarar 2017 hukumomin Najeriya suka haramta kungiyar ta IPOB tare da saka ta cikin jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda saboda fito-na-fito da suke yi da jami’an tsaro.

Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi

Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:05 0:00

XS
SM
MD
LG