Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DSS Na Neman Igboho Ruwa A Jallo, Ta Kama Makamai A Samamen Da Ta Kai Gidansa


Sunday Igbohon (Twitter/ Sunday Igbohon)
Sunday Igbohon (Twitter/ Sunday Igbohon)

“Muna kira ga Adeyemi/ Igboho da ya mika kansa ga ofishin jami’an tsaro mafi kusa. Sannan masu yabon sa, su ba shi shawara da ya yi abin da ya kamata. Ya mika kansa ga hukumomi.”

Jami’an tsaron hukumar DSS sun kai samame gidan Sunday Adeniyi Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, lamarin da ya kai ga musayar wuta har mutum biyu daga cikin "‘yan bindigarsa" suka mutu.

An kai samamen ne a ranar Alhamis a gidansa da ke birnin Ibadan na jihar Oyo a kudu maso yammcin Najeriya a cewar wata sanarwa da hukumar DSS ta fitar sanye da sa hannun kakakinta Peter Afunanya.

Makaman da aka kama a gidan Igboho (DSS)
Makaman da aka kama a gidan Igboho (DSS)

“Mun kai samamen ne bisa wasu bayanan sirri da muka tattaro, wadanda suka yi nuni da cewa ya tara dumbin makamai a gidan.

“Muna dosar gidan, wasu mutane su tara wadanda muke zargin masu gadin Igboho ne, suka budewa tawagar jami’anmu wuta da bindiga, shida daga cikinsu suna dauke da bindiga kirar AK 47 wasu uku kuma suna da kananan bindigogi.” A cewar sanarwar.

Sai dai Afunanya ya ce, Igboho, wanda ke gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa, ya yi amfani da lokacin da ake musayar wutar ya tsere daga gidan.

Makaman da aka kama a gidan Igboho (DSS)
Makaman da aka kama a gidan Igboho (DSS)

“Musayar wutar, wacce aka kwashe sa’a daya ana yi, ta ba Igboho damar arcewa, yanzu Sunday Adeyemi wanda ake wa lakabi da Sunday Igboho na tserewa hukuma.

“Ta yiwu ya yi ta gudu iya yadda yake so, ko ya yi ta buya. Amma ya kwan da sanin cewa hukuma za ta tarar da shi.” In ji kakakin na DSS.

An Kashe Biyu Daga Cikin Masu Gadin Igboho

A cikin sanarwar, kakakin na DSS Afunanya ya kara da cewa, a lokacin da aka fara musayar wutar, an kashe biyu daga cikin mutanen Igboho wadanda ke dauke da makamai, sannan an kama sauran.

Kayayyakin da aka kama a gidan Igboho (DSS)
Kayayyakin da aka kama a gidan Igboho (DSS)

“Sai dai daya daga cikin jami’anmu ya ji rauni bayan da wani daga cikin maharan ya harbe shi a hannun dama. Amma an ba shi kulawa kuma yana samun sauki.”

“Muna kira ga Adeyemi Igboho da ya mika kansa ga ofishin jami’an tsaro mafi kusa. Sannan masu yaba mai, su ba shi shawara da ya yi abin da ya kamata. Ya mika kansa ga hukumomi.” In ji Afunyaya.

Makaman Da Aka Samu A Gidan Igboho

Daga cikin makaman da aka kama a cewar hukumar ta DSS, “akwai bindigogi AK 47 guda bakwai, kananan bindigogi uku, madaukin harsashai guda 30, harsashai dubu biyar masu tsirin mita 7.62, adduna biyar, kananan bindugogi pistol 2 da abin hangen nesa daya.”

Baya ga haka hukumar ta samu layu, abin magana na tafi da gidanka, kwafutoci na tafi da gidanka da paspo din Igboho da na sauran mutanensa.

Mutanen Da Aka Kama A Gidan Igboho

Hukumar ta DSS ta kara da cewa ta kama mutum 13 da suka hada da maza 12 da mace daya wadanda duk an tafi da su Abuja.

Ga sunayensu kamar yadda hukumar ta DSS ta fitar:

Abdulateef Ofeyagbe, Amoda Bbatunde wacce ake kira Lady K (mace), Tajudeen Erinoyen, Diakola Ademola, Abideen Shittu, Jamiu Noah, Ayobami Donald, Adelabe Usman, Oluwafelumi Kunle, Raji Kazeem, Taiwo Opeyemi, dda kuma Bamidele Sunday.

A cewar hukumar ta DSS, wannan kame da makamai da aka samu a gidan Igboho, alama ce ce da ke nuni da cewa akwai wata makarkashiya da yake shiryawa tare da yaransa don yin tawaye ga hukumomin Najeriya.

Wasu daga cikin kayayyaki da makamai da aka kama a gidan Igboho (DSS)
Wasu daga cikin kayayyaki da makamai da aka kama a gidan Igboho (DSS)

Karin bayani akan: Nnamdi Kanu, Igbo, Biafra, Biyafara, DSS, IPOB, Abuja, Nigeria, da Najeriya.

“Muna so mu sanar da ‘yan Najeriya da duniya baki daya cewa, Sunday Igboho da kungiyarsa wadanda suke fakewa da fafutukar cin gashin kansu, sun tara makamai don su haifar da rudani a tsakanin al’uma.”

Wannan samame da aka kai kan gidan Igboho na zuwa ne kasa da kwana biyu kafin wani gangami da zai jagoranta a Legas, wanda za a yi don neman kafa kasar Yarbawa.

Sai dai daga baya, Igboho ya soke taron bayan wannan samamen da aka kai masa.

A watan Afrilu gboho, ya taba ikirarin cewa sojoji sun kai samame gidansa, amma rundunar sojojin ta musanta wannan zargi.

A baya, rahotanni da dama sun ruwaito Igboho yana ba Fulani da ke yankin jihar Oyo wa'adin su fice daga jihar, saboda abin da ya kira matsalolin tsaro da suke haifarwa, wadanda suka hada da kai hare-hare da yin garkuwa da mutane, zargin da Fulanin suka musanta.

Igboho ya sha fadin cewa fafutukar da yake ta kare al'umar Yarbawa ce da kwato masu hakkinsu, abin da hukukomi suka ce yana wuce gona da iri saboda daukan doka da yake yi a hannunsa.

Harin da aka kai gidan Igboho na zuwa ne, kwana hudu bayan da hukumomin kasar suka cafke shugaban kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Biafra Nnamdi Kanu, wanda ake kan yi masa shari'a kan cin amanar kasa.

Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi

Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:05 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG