Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nnamdi Kanu: Abin Da Mutane Ke Cewa Kan Kiran IPOB Na A Kauracewa Kayayyakin Kenya


Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta.
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta.

A farkon makon nan kungiyar ta IPOB ta yi yakuwar mambobinta ta kauracewa kayayyakin kasar na Kenya saboda rawar da ta zarge ta da taka wa wajen kama Nnamdi Kanu.

Kiran da kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB ta yi wa mambobinta da ma dukkanin 'yan kabilar Igbo da su kaurace wa kayayyakin da aka kirkiro a kasar Kenya da ke gabashin Afirka, yanzu yana bazuwa ainun a kudu maso gabashin Najeriya, wani lamarin da ke ta jan hankalin jama'a, musamman masharhanta da masana.

Kungiyar IPOB ta yi wannan kira ne a farkon wannan makon, da zargin cewa kasar Kenya tana da hannu a kame jagoranta Mazi Nnamdi Kanu da gwamnatin Najeriya ta yi, wani zargin da gwamnatin kasar Kenya ta riga ta musanta.

"Damuwa ta ita ce ban san kayayyakin da ke shigowa daga kasar Kenya ba. Na dai san cewa a da muna samun Kiwi daga kasar Kenya. Amma ina marhaba lale da duk abin da za a yi a nuna fushi da rashin amincewa da abin da kasar Kenya ta yi," in ji Mista Justin Onuaha da ke sharhi kan al’amutan yau da kullum.

Karin bayani akan: Nnamdi Kanu, Uhuru Kenyatta, IPOB, Biafra, Kenya, Nigeria, da Najeriya.

A cewar Mista Chinedu Onyeje, "maganar cewa a kaurace wa kayayyakinsu bai dace ba, kuma ba zai haifar da wani sakamako mafi a’ala ba."

"Idan kasar Kenya tana dogara ne da Najeriya, toh wannan zai yi tasiri. Amma ka tuna cewa adadin 'yan IPOB kadan ne, kuma ba kowa ne zai bi wannan maganarsu ba, saboda ba kowane Igbo ne ke wannan ra'ayinsu ba. Ba zai yi tasiri bisa wadannan dalilan ba." In ji Dakta Emmanuel Okechi

Sai dai Dakta Celestine Nwosu yana mai cewa wannan matakin da kungiyar ta dauka zai shafi tattalin arzikin kasar Kenya sosai.

"Tabbas zai shafi tattalin arzikinsu sosai, saboda idan abin da muke ji gaskiya ne cewar kungiyar IPOB tana da mabiya sama da miliyan arba'in a fadin duniya, wannan matakin zai shafi tattalin arzikin kasar Kenya sosai." A cewar Nwosu.

Yanzu kayayyakin da kasar Kenya ke tura Najeriya sun fadi warwas zuwa dala miliyan 33 a shekarar 2015, daga dala milyan 37 a shekarar 2008, inji ofishin kididdiga na kasar Kenya, wani al'amari da ke nuni da cewa akwai kyakkyawar dangantakar kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi

Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:05 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG