Kungiyar ‘Yan Wasan Najeriya U-23 Zasu Fara Shirin Wasannin Olympic

Nigeria's head coach Samson Siasia, left, and his team members celebrate after defeating Belgium 4-1 in a men's semifinal soccer match between Belgium and Nigeria at the Beijing 2008 Olympics in Shanghai, Tuesday, Aug. 19, 2008. (AP Photo/Eugene Hoshiko)

Kungiyar matasa masu ‘kasa da shekaru ashirin da uku wato U-23, zasu fara shirye shiryen su a karon farko cikin watan Fabarairu, gabannin wasannin Olympic din shekara ta 2016.

Koch Samson Siasia ne ya fadi haka, inda yake cewa “zamu fara shirye shiryen mu cikin watan Fabarairu, da fatan duk kungiyoyin da ‘yan wasa suke zasu saki ‘yan wasansu akan lokaci. Tun da mun san yadda wasannin Olympic suke.”

Ya ci gaba da cewa mun gane cewa kungiyoyi na bukatar ‘yan wasansu, amma wannan kuma aikin kasa ne.

Siasia yace ina mai matukar farin ciki kan kokarin da mukayi a wasannin AFCON U-23 da akayi a kasar Senegal da kuma samun shiga wasannin Olympic. Mun sami sakonnin yabo daga ‘yan Najeriya.

Najeriya dai ta samu nasarar zama zakaran a wasannin Olympic na shekara ta 1996 ta kuma samu lambar yabo ta Silver a Olympic din da akayi a Beijing ta shekara ta 2008, Najeriya da Algeria da Afirka ta Kudu sune zasu wakilci Afirka, ita kuma Senegal zata kara a wasannin tantancewa na shiga wasannin Rio.