Lionel Messi, dan wasan Barcelona, ya lashe lambar yabo na dan kwallon da yafi kowane dan kwallo taka leda a duniya, ya doke Cristiano Ronaldo, da wasu fitattun ‘yan wasa,a wani biki da aka aka gudanar a Dubai.
Da yake jawabi Messi yace ya jidadin wannan kyautar amma a cewarsa wannan nasara ce ga Barcelona da daukacin ‘yan wasan kungiyar.
Lionel Messi, ya taka rawar gani domin ya jagoranci Barcelona, ta lashe kyaututuka 5, da lashe kofin duniya na kungiyoyin kwallon kafa, ranar lahadin da ta gabata, haka kuma Barcelona ta lashe kyautar kungiyar da tafi kowace kungiya iya taka leda a duniya.
A wannan shekarar Lionel Messi, ya taka leda sau 60, tsakanin bugawa kasar sa Argentina, da klub dinsa, Barcelona, ya kuma jefa kwallaye 61, a raga.
Ana harsahen za’a baiwa Lionel Messi, fan na Ingila, 400,000, a kowane sati inda ya amince ya koma Manchester City.