Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikici Na Neman Sake Barkewa A Hukumar Kwallon Kafar Najeriya


Nigeria Cabinet
Nigeria Cabinet

Ana cigaba da samun hatsaniya a cikin hukumar kwalon kafar kasar Najeriya, a dai-dai lokacin da Chris Giwa ke yunkurin bayyanar da kanshi a matsayin shugaban kungiyar ‘yan wasan.

Amma dai ministan Matasa da wasannani Solomon Dalung, ya gargade shi da cewar kada ya kawo wata hatsaniya a cikin kungiyar, ganin cewar ‘yan wasan na shirye-shiryen wasan zakaru nashekara 2016.

Mr. Giwa, ya cigaba da haklikancewa a kan shine shugaban da aka zaba na hukumar kwallon kafar Najeriya. Kuma ya mika takardar koken shi ga ministan matasa da wasanni.

Ministan matasa da wasannin Mr. Solomon, ya kara da cewar, ya lura ana mulkin danniya a cikin hukumar kwallon kafar Najeriya, wajen warware wasu matsalolin cikin gida, amma a matsayin shi na mutun mai son gaskiya kuma ministan matasa da wasanni, zai kokarta wajen ganin an warware duk wasu matsaloli cikin lumana da fahimtar juna.

Wannan tsarin nawa kada a dauke shi a matsayin gazawa, wannan wata hanya ce da za’a samu jituwa a tsakanin jama’a. Haka kuma nasha fade bazan yi katsalandan a harkrar kungiyar ba amma ina nan akan duk wani abu na gaskiya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG