Dan kwallon kasar Kamaru, Samuel Eto’o yayi hasashen cewa dan tamaula na kasar Brazil, Neymar, shine zai zamo zakaran kwallon kafa a duniya nan gaba a bayan Lionel Messi da Cristiano Ronaldo sun gama yayinsu.
Neymar ya jefa kwallaye 70 a raga a wasanni 134 da ya buga ma FC Barcelona tun komawarsa kulob din daga Santos ta Brazil a 2013.
Dan wasan na gaba, ya shiga cikin wadanda suka yi takarar kambun zakaran kwallon kafa na duniya a bayan da ya taimakawa kulob dinsa wajen lashe dukkan manyuan kofuna 3 da ta yi takararsu a shekarar da ta shige.
Eto’o ya fadawa gidan telebijin na ESPN Brazil cewa Neymar na iya zamowa dan kwallon kafa fiye da kowa a duniya. Yace a bayan Messi da Ronaldo sun gama yayinsu, lallai Neymar zai zamo na daya a duniya.
Sai dai kuma, y ace “ya kamata Neymar ya san cewa kusan komai ya dogara ne a kansa. Ya kamata ya san cewa yana da basirar kwallon kafa, amma dole ne ya rika furatis a koyaushe. Ba kowa ne ke da irin basirarsa ta kwallo ba.”
Yaci gaba da cewa “Shekarun Neymar 24 ne kawai, na grime shi da shekaru 10, amma ana daukarsa a zaman jagora a kasar Brazil. A saboda irin basira da kwarewarsa, zai iya bada shawara gad an wasa mai shekaru 35 da suke buga kwallo tare.”