Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ra'ayoyin Samari, Akan Anfani Da Turare Tsakanin Samari Da 'Yan Mata


A shirin mu na wannan makon mun sami zantawa ne da wasu samari daga wurare daban daban inda suka bayyana mana ra’ayoyin su agame da wadanda suka fi anfani da turare tsakanin samari da ‘yan mata da kuma dalilin da yasa hakan.

Kamar yadda masu iya Magana suka ce sawun giwa ya take rakumi, dalilin wannan Magana kuwa itace kusan kashi tamanin na samarin da suka tofa albarkacin bakin su sun tabbatar da cewa lallai mata sun fi anfani da turare kamar yadda wani saurayi y ace mata ‘yan kwalliya ne, dan haka turare wajibi ne garesu.

Da muka cigaba da jin ra’ayoyin samarin dangane da dalilan da suke sa mata anfani da turaren sai suka nuna cewar saboda halittar da Allah subuhanahu wata’ala yayi masu, da kuma irin sinadarin da jikin su ke fitarwa, ya zama wajibi su kiyaye domin kauce ma warin jiki.

Yawanci jikin dan’adam yakan fitar da sinari iri daban daban kama daga zufa da sauran su wadda ya kamata duk wanda yayi zufa yayi wanka domin tsabtace jikin sa wanda rashin hakan ke sa jiki ya fara wari.

Saurari cikakkiyar hirar a nan…Dandalinvoa.com

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG