Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Emmanuel Amuneke Zai Bar Golden Eaglets


Kwach din ‘yan wasan kwallon kafa masu kasa da shekaru 17 Emmanuel Amuneke ya ce bashi da ra’ayin cigaba da aiki da kungiyar ‘yan wasan Golden Eaglets.

Tsohon kocin ne ya jagoranci kungiyar ‘yan wasan a shekarar 2015 inda suka sami nasarar lashe kofin duniya na hukumar FIFA na ‘yan kasa da shekaru 17 da aka buga a Chile, kuma a yanzu haka yana neman chanza sheka.

A wata hira da yayi da gidan radion Nigeria Info FM, kocin ya bayyana cewa ya dade da rike irin wannan matsayin dan haka yace gaskiya ba zai iya cigaba da jagorancin kungiyar ba.

Amuneke ya kara da cewa, dole ne mutum ya nemi cigaba domin ganin yadda gaba zata kasance.

Emmanuel Amuneke ne ya gaji Manu Garba a matsayin babban kocin kungiyar ta ‘yan kasa da shekaru 17 a shekarar 2013.

Haka kuma idan muka garzaya Nigerian Professional Football League Chanpions Eyimba, kocin kungiyar Kadiri Ikhana, shima ya ajiye aiki.

Hukumomin kungiyar sun tabbatar da cewar dama baza a sake sabunta kwangilar tsohon shugaban ba baya ga nasarar da kungiyar ‘yan wasan ta samu a karkashin jagorancin sa a watan da ya gabata.

Baza a iya kara wa’adin Kwangilar Kadiri Ikhana ba, kungiyar ta yanke hukuncin kawo wani sabon shugaba a wasu ‘yan kwanaki masu zuwa wanda zai maye gurbin tsohon shugaban a wani sakon da mai Magana da yawun kungiyar mr Farrie Alaputa ya aika ta shafin yada zumunta na twitter.

Rahotanni na nuna cewar yanzu haka kungiyar ta fara zawarcin mataimakin kocin ‘yan wasan Super Eglets Salisu Yusuf domin zan ragamar kungiyar.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG