Kungiyar 'Yan Kwadago Ta CLOGSAG Ta Fara Yajin Aiki A Ghana

ma'aikatan gwamnatin Ghana karkashin kungiyar yan kwadago ta CLOGSAG

A ranar Alhamis ne dubban ma'aikatan gwamnatin Ghana karkashin kungiyar 'yan kwadago ta CLOGSAG suka fara yajin aiki a sassan fadin kasar abin da ya sanya mabukata a ofis ofis din gundumomin kasar cikin halin damuwa.

Kungiyar ma'aikatan gwamnati na bukatar da a ringa biyansu alawus alawus din yan baruwanmu wato alawus da zai kawar da hankullansu ga barin shiga siyasa. Hakan ya fara janyo koma baya sosai ga harkokin samar ma aluman kasar wasu muhimman abubuwan da suke bukata kamar takardun sheda na kasuwanci da na haihuwa da dai sauransu.

Wani saurayi da ya yi ikrarin rejistar harkar kasuwanci a fadar Rejista Janar din kasar ya isa ya tarar da ofis din a rufe. Obed Kofi Annan ya ce, 'Na isa domin karbar takardar shaidar kasuwanci na to sai mai gadi ya ce ma'aikatan duk suna yajin aiki a don haka ban samu ba.'

Daya daga cikin mambobin kungiyar yan kwadagon a gundumar Tepa, Mallam Sani Ceeba, ya bayyana cewa gwamnati ta amince da bukatar amma bata cika alkawalin samar musu da wannan alawus dinba

Mallam Sani Uzairu tsohon babban jami'i a gundumar Asokore Mampong kana mai nazari bisa harkokin ma'aikatan gwamnati yau da kullum inda yake cewa yajin aikin ma'aikata ya sanya gwamnati hasarar kudaden shiga da ake samu a gundumomin fadin kasar amma mafi a'ala itace da akara albashin ma'aikatan.

A nasa jawabi Mataimakin Ministan ma'aikata a kasar, Bright Wereko Brobbey, ya tabbatar da ikrarin kungiyar tare da cewa rashin kudi yabyi sanadin jinkirin samar musu da alawus din amma suna tattaunawa da shugabannin kungiyan domin cimma daidaituwa.

A baya bayannan ne babbar kotun kolin kasar ta zartas da hukuncin haramta wa ma'aikata karkashin kungiyar yan kwadago ta CLOGSAG shiga siyasa abinda ya ba su damar bukatar da su kuma a basu alawus muddan an hana su alakanta kansu da wata jamiyya.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Yan Kwadago Ta Clogsag Ta Fara Yajin Aiki Aghana