La’akkari da matsalar man fetur da ta shafi ɓangarori da dama a Najeriya, kungiyar kwadago ta NLC a kasar ta bayyana cewa akwai iyaka a wahalar da 'yan Najeriya za su iya jurewa fuskanta a wannan yanayi.
Comrade Nasir Kabir, Sakataren tsare-tsare na hadaddiyar kungiyar, ya ce kungiyar ta fito ta yi tir da wannan matsalla da ake ciki kuma kafin kungiyar ta dauki wani matsaya, sai ta kira ko ta ja hankalin gwamnati don ta fahimci cewa ga hanyoyin da ya kamata a bi don magance matsaloli, kuma idan ta ki, to za su dauki mataki da ba zai yi wa gwamnati dadi ba.
Sai dai a cewar Ƙwararre a harkar man fetur kuma shugaban kamfanin Skymark Energy and Power Limited a Najeriya, Alhaji Mohammed Saleh Hasan, wannan ba lokaci ba ne na harzuka mutane domin matsalar tana da nasaba da tashin da farashin man fetur ya yi a kasuwannin duniya.
Baya ga karanci da kuma tsadar man fetur, akwai tsadar bakin man dizil da ake fama da shi a yanzu, sai kuma karancın man jıragen sama dake neman durkusar da harkan sufurın jıragen sama a kasar ında kamfanonın sufurın jırage suka yı barazanar fara yajın aıkı, baya ga matsanacın karancın wutan latarkı da kasar ke fama da shi a halin yanzu.
Sai dai kwararre kan harkar sufurın jıragen sama, Injiniya Balamı Issac David ya ce dole a fito a yi wa jama’a bayani da za su fahimta.
Alkaluma sun nuna cewa farashin kayan masarufi sun tashi a kasuwanni kuma hakan na da alaka ne da tsadar fetur da dizil wanda litarsu ta zarce N250 da N700.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: