Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar NLC Ta Yi Watsi Da Shirin Gwamnatin Najeriya Na Kara Haraji Kan Lemun Kwalba


Shugaban NLC, Ayuba Wabba, a wajen taron
Shugaban NLC, Ayuba Wabba, a wajen taron

Kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC ta yi watsi da shirin gwamnatin Najeriya na kara haraji kan lemun kwalba wanda ake cewa carbonated drinks a turance.

Kungiyar NLC ta bayyana matsayin ta ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Kwamared Ayuba Wabba, wadda aka raba wa manema labarai a birnin tarayya Abuja da ranar Juma’ah..

Gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa ta na shirin yin karin harajin a matsayin wata hanya ta hana shan sukari fiye da kima, duban kiba, da kuma samar da karin kudaden shiga don samar da kasafin kudin shekarar 2022 kamar yadda ministar Kudi Zainab Shamsuna Ahmed ta bayyana.

Sai dai kungiyar NLC ta yi imanin cewa aiwatar da karin haraji kan abubuwan sha da ba na barasa musamman lemun kwalba da ake cewa carbonated drinks a turance, wanda yana daya daga cikin tanade-tanade a cikin dokar kudi ta shekarar 2021, zai kara sanya talakawa cikin matsi ne.

Don haka ne kungiyar NLC ta bukaci majalisar dokokin kasar da ta gaggauta yiwa sashes dokar kudin ta shearer 2021 gyarar fuska wanda ta sake bullo da harajin haraji kan abubuwan sha da ba na barasa ba.

A ranar 31 ga watan Disambar shekarar 2021 ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar kasafin kudin ta shearer 2021.

Wasu daga cikin tanade-tanaden dokar kudin dai sun hada da sanya haraji kan abubuwan sha da ake samarwa a cikin gida wadanda ba na barasa ba masu sikari.

Gwamnatin Najeriya dai ta kafa dalilinta na daukan wannan mataki kan hana shan yawan sikari da ‘yan Najeriya ke yi saboda hakan na haifar da kari a adadin masu kiba da ciwon sukari.

A cikin wata wasika mai dauke da ranar 27 ga watan Nuwambar shekarar 2021, kungiyar kwadago ta Najeriya ta rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, da shugabannin majalisun dokokin kasar guda biyu tana rokon gwamnati ta dakatar da yin hakan don gudun jefa yan kasar cikin karin matsin tattalin arziki.

XS
SM
MD
LG