Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NLC Ta Janye Shirinta Na Yin Zanga-zanga A Najeriya

Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba yana jawabi a lokacin zanga-zangar da suka yi a Kaduna a bara (Twitter/NLC)
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC, Ayuba Wabba yana jawabi a lokacin zanga-zangar da suka yi a Kaduna a bara (Twitter/NLC)

A farkon makon nan gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa ta janye shirin cire kudaden tallafin mai.

Kungiyar kwadago ta NLC a Najeriya ta janye shirinta na gudanar da zanga-zanga don nuna adawa da shirin gwamnati na janye tallafin man fetur.

Wata sanarwa da shugaban kungiyar Comrade Ayuba Waba ya fitar a shafin kungiyar ta NLC a ranar Talata, ta ce sun janye shirin yin zanga-zanga ne bayan da gwamnatin tarayya ta sauya matsayarta.

A cewar Waba, a karshen watan Nuwambar bara, gwamnati ta ayyana shirinta na janye tallafin mai, abin da ke nuni da cewa za a kara farashin mai a kasar.

“Bayan janyewa da ta yi, kwamitin gudanarwar kungiyar ta NLC ya yi taron gaggawa da wannan safiya (Talata,) Bayan tattaunawa, mun dauki matsayar janye shirin gudanar da zanga-zangar ta ranar 27 ga watan Janairun 2022 da kuma wacce za a yi a ranar 2 ga watan Fabrairun 2022.” In ji Comrade Waba.

Waba ya kara da cewa tuni an isar da wannan sako na janye zanga-zangar ga “kawaye” kungiyoyin fararen hula.

A farkon makon nan gwamnatin tarayyar ta bayyana cewa ta janye shirin cire kudaden tallafin mai.

XS
SM
MD
LG