Kungiyar Kasashen Afirka Ta Cika Shekaru Hamsin da Uku da Kafawa

Janar Yakubu Gowon, tsohon shugaban Najeriya na cikin shugabannin Afirka da suka reni kungiyar kasashen Afirka da ta fara da suna OAU kafin ta zama AU

Janar Yakubu Gowon, tsohon shugaban Najeriya na cikin shugabannin Afirka da suka reni kungiyar kasashen Afirka da ta fara da suna OAU kafin ta zama AU

Shekaru hamsin da uku da kafa kungiyar kasashen Afirka ke nan, shin kasashen na iya dunkulewa su zama kasa daya saboda burin kafata ke nan a lokacin Shugabanni irin su Kanar Ghaddafi na kasar Libya

Bayan wasu 'yan shekaru akan samun alamar nasarorin manufofin da suka kaiga kirkiro da kungiyar kasashen Afirka shugabannin Afirka sun canzawa kungiyar manufofi inda yanzu ta zama AU.

Dangane da nufin samun dunkule kasashen zuwa kasa daya tilo Farfasa Ado Muhammad masanin tarihi ne kuma shugaban jami'ar Tawa yace kungiya ce inda shugabannin ke kare kansu. Ba jama'arsu suke karewa ba. Abun da suka sa gaba shi ne yadda zasu cigaba da iko ko yadda zasu sake kundun tsarin mulki domin su cigaba da iko. Yace basu san lokacin da ya kamata su hakura ba. Irin abun da ya samu Blaise Campaore shugaban Bokina Faso ke nan. 'yan kungiyar basa tsawtawa juna ko su dauki matakin gaggawa idan lamari ya baci

Yace kare kansu su keyi suna zuwa suna kare juna. Su kan kuma debi kudaden kasashensu su aika wata kasa domin kare shugaban.Kasa kamar Najeriya ta ba kasashe da dama kudi domin taimakawa shugabanninsu.

Sedeo Abdu wani matashi mai akidar yaki da 'yan jarin hujja nada irin ra'ayin Farfasa Muhammad. Yayi misali da kasashen renen Faransa da na Birtaniya. Yace jayayya ke tsakaninsu. Da irin jayayyar dake tsakaninsu ta yaya zasu dunkule. Yadda Faransa take jan kasashe renenta haka ma Birtaniya ke yi. Saboda haka babu yadda zasu zama kasa daya.

To sai dai Farfasa Ado Muhammad yace har yanzu yana da kwarin gwuiwar yiwuwar kasashen zasu iya hadewa amma sai an samu shugabannin kasashe gwarzaye wadanda zasu dage kan abun da suka kudura kamaN Shugaban Najeriya Muhammad Buhari.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Kungiyar Kasashen Afirka Ta Cika Shekaru Hasin da Uku da Kafawa - 3' 03"