Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Zasuyi Kasa A Guiwa Ba Wajen Tabbatar Da Tsaron


Kakakin 'Yan Sanda Kaftin Mainassara Adili Toro
Kakakin 'Yan Sanda Kaftin Mainassara Adili Toro

Za’a ci gaba da daukar'yan Sanda domin tabbatar da tsaron lafiyar jama’a da dukiyar su

A jamhuriyar Nijar yau aka yi bukin yaye wasu dalibai ‘yan sanda kimanin 1522 da aka kammala horos da su na tsawon watanni 18 a fannin aikin tsaro da bincike da kwantar da tarzoma a ci gaba da kara daukar matakan tsaron da hukumomin kasar suka sa gaba don dakile matsalar tsaron da ake fama da ita a ‘yan shekarun nan.

Wadannan sabbin ‘yan Sanda sun hada da kwamishinoni ashirin da takwas da hafsoshi hamsin da uku da sufeto dari biyar da goma sha biyu da jami’an kwatar da tarzoma kimanin dari tara da ashirin da daya akwai kimanin mata tama'nin, yayin da aka bayana cewa hudu daga cikin su suka rasa rayukan su a dalilan rashin lafiya ko kuma hatsarin da suka ci karo da shi a lokacin da suke daukar horo.

Kakakin hukumar ‘yan Sanda kaftin Mainasara Adili Toro, ya baya cewa bisa la’akari da yanayin da ake ciki a yau za’a ci gaba da daukar ma’aikata domin tabbatar da tsaron jama’a da dukiyar su domin kuma ganin yadda kasa ke kara bunkasa.

Kaftin Toro, ya kara da cewa ‘yan Sanda ba zasuyi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da tsaron rayukan jama’ar kasar Nijar, a kowane lokaci.

Wannan it ace rundunar ‘yan Sanda mafi yawan jami’ai, da aka horar a wanna makaranta tun kafa a 1965, kuma a cewar daraktan makarantar Muhammad Lawali Madugu, yana da cikakkiyar yarda da abubuwan da aka koyar da wadannan sabbin ‘yan Sanda domin tabbatar da tsaro yaki da ta’addanci, yaki da masu fataucin makamai da muyagun kwayoyi kula da sha’anin sufiri da sauran su.

XS
SM
MD
LG