Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Malaman Jami'o'in Sudan ta Kudu Zasu Fara Yajin Aiki Yau


Mataimakin Shugaban kasa Riek Machar da Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir
Mataimakin Shugaban kasa Riek Machar da Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir

A Sudan ta Kudu malamai a jami'o'in kasar biyar sunyi barzanar zasu fara yajin aiki yau Laraba, idan gwamnati bata biya albashinsu na watanni uku d a suka shige ba, da kuma wasu alawus alawus da suke bin gwamnati tun bara.

Karamin minista mai kula da ilimi mai zurfi yace ma'aikatarsa tana sane da bukatar da ma'aikatan jami'o'in suka gabatar, amma gwamnatin kasar tana cikin matsanancin karancin kudi,bata da halin samun kudi domin biyawa ma'aikatan bukatunsu.

Jiya Talata waklan ma'aikatan jami'o'in kasar biyar suka kira taron manema labarai a Juba, babban birnin kasar inda suka bada sanarwar zasu shiga yajin aiki.

Kakakin kungiyar ma'aikatan jami'o'in Sudan ta Kudu, Phillip A Finish Apollo, wanda har wayau shine wakilin kungiyar malaman jami'o'i dake Juba. Yace daukacin malaman jami'o'in kasar daga yau Laraba 25 ga wata, ba zasu je bakin aiki ba, har sai ma'aikatar kudin kasar ta biya dukkan bashin da suke bin gwamnati, sannan ta fara aiwatar da sabon tsarin albashi kamin su koma bakin aiki.

XS
SM
MD
LG