Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Zambia zata gudanar da zabukanta watan Agusta mai zuwa


Shugaban Zambia na yanzu Edgar Lungu
Shugaban Zambia na yanzu Edgar Lungu

Watan Agusta mai zuwa ne kasar Zambia zata gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki da na kananan hukumomi kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.

Yau Ltinin hukumar zaben kasar Zambia tace za'a fara yakin neman zaben shugaban kasa da na wakilan majalisar kasar da shugabannin kananan hukumomi da za'a yi a watan Agusta idan Allah Ya kai rai.

Shugaban hukumar zaben mai shari'a Esatu E. Chulu ya kaddamar da binciken rajistan zabe na wucin gadi.

A lokacin da ake shirin zaben an bukaci wadanda suka cancanta yin zaben su tabbatar da gaskiyar bayanansu a rajistan zaben na wucin gadi kafin a tsara sunayensu a rajistan din-din-din

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG