Ma'aikatar harkokin wajen Amurka tace wakilan Amurka sun fice daga bikin saboda kasancewar Shugaban Sudan Omar al-Bashir wanda kotun kasa da kasa na manyan laifuka dake Hague ta tuhuma da laifin kisan kare dangi da ya yi a yankin Dafur cikin Sudan din.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka tace Amurka ta damu cewa Shugaba Bashir ya iya balaguro zuwa Uganda, kasar da take cikin kotun kasa da kasa ko ICC. Kasancewa tana cikin kotun kamata ya yi ta tsareshi ta kuma mikashi ga kotun. Ba shi kadai ba duk wanda kotun ke zarga da wani laifi idan har ya shigo kasarta yakamata ta mikashi ga kotun ne. Maimakon hakan Museveni a jawabinsa jiya Alhamis ya fito fili ya nuna wa kotun bakin raini.
Da yake yiwa shugabannin Afirka jawabi, Museveni yace shi yanzu ya dawo daga rakiyar kotun domin cike take da mutanen banza mutanen wofi marasa imani. Da ya yi wadannan kalamun ne wakilan Amurka da Canada da na tarayyar turai suka fice.
Wannan wa'adin mulki shi ne na biyar da za'a rantsar da shugaban wanda ya kama madafin ikon kasar a shekarar 1986.