Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Sojin Masar Ta Kai Hari Akan Sansanin ISIS dake Zirin Sinai


Shugaban Kasar Masar ei-Sissi
Shugaban Kasar Masar ei-Sissi

Ahalinda ake ciki kuma rundunar sojojin Masar yanzu haka sun kai farmaki kan mayakan sakan ISIS dake zirin Sinai,kamar yadda aka ji daga bakin babban hafsan hafsoshin mayakan Amurka Janar Joe Dunford. Dunford ya fadawa wasu manema labarai kalilan dake tare da shi cikin jirgin sojan Amurka kan hanyarsa zuwa Amurka daga birnin Brussels, a jiya Alhamis.

Dunford ya bayyana fatar samun sakamakon harin da sojojin na Masar suka kai bayan ya sauka a Amurka. Amma bai bada wanin karin bayani ba.

Amurka tana kiyasin cewa akwai daruruwan mayakan sakai 'yan ISIS, ko ma yawansu ya kai dubu daya a zirin na SINAI.

Haka nan akwai mayakan sakai 'yan Bedouin a zirin na SINAI, wadanda suke hada kai da ISIS, inji Janar Dunford.

Rundunar sojojin Amurka tace ta fara ganin dangantaka tsakanin mayakan sakai da suke zirin na Sinai da mayakan sakai na ISIS a fadin gabas ta tsakiya, wadanda a baya take kallonsu a zaman daban.

Dunford yace, "munga dangantaka ko sarsala tsakanin ISIS da take SINAI da kuma Raqqah," a maganar da yayi da manema labaran. "Munga tuntubar juna tsakanin 'yan ISIS a Sinai da kuma takwarorinsu dake Libya, da kuma a wasu wurare, saboda haka muna sa ido akai sosai."

Rahotannin farmakin da sojojin Masar suka kai kan mayakan ISIS a Sinai, yana zuwa ne a kuma dai dai lokacinda Amurka da NATO suke tunanin horaswa da kuma samar da makamai ga mayaka a Libya.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG