Da farko dai an gurfanar da tsohon gwamnan ne a wata kotun majastare da ke Dutse, babban birnin Jihar ta Jigawa, inda masu shigar da kara suka ce ya yi kalaman tunzura magoyo bayan nasa ne a wajen wani gangamin siyasa da jam`iyyarsa ta PDP ta yi a jihar Jigawar.
Sai dai bayan fara sauraron shari`ar, lauyan da ke kare Sule Lamido, Barista Yakubu Ruba ya kalubalanci kotun cewa ba ta da hurumin sauraron karar. Yana mai cewa ba a bi tsarin doka ba wajen shigar da karar.
Amma alkalin kotun majistare, mai shari`a Usman Mohammed Lamin ya yi watsi da wannan uzuri, saboda a cewarsa babu wata saba ka`ida.
Dangane da haka ne Lauya mai kariya, Yakubu Ruba ya daukaka kara zuwa babbar kotun jihar, inda ya nemi kotun majistaren ta dakatar da ta ta shari`ar har sai abin da hali ya yi.
A nata hukuncin, babbar kotun jihar, wadda masu shari`a Ahmed Musa Gumel, da Umar Sadiq da kuma Abdulhadi Suleman suka jagoranci zaman, sun sallami tsohon gwamnan, sannan suka yi watsi da duk tuhumar da ake masa kamar yadda lauyansa ya bukata tun farko.
Gwamnatin APC mai mulki jihar Jigawa a nata bangaren, tace ba ta za ta daukaka kara a kan wannnan hukuncin da babbar kotun ta yanke kamar yadda mai magana da yawun gwamna Badaru Abubakar, Mallam Mohammed Bello Zaki ya tabbatar wa Muryar Amurka.
Alhaji Sule Lamido dai guda ne cikin masu neman takarar shugabancin Najeriya a karkashin babbar jam`iyyar adawa ta PDP. Kuma tun lokacin da aka zarge shi da yunkurin tada-zaune-tsaye, magoya bayansa ke zargin gwamnati da yunkurin yi wa jagoran nasu bi-ta-da-kulli da nufin murkushe adawa, amma gwamnatin ta musanta.
Your browser doesn’t support HTML5