Gwamnatin jihar Niger ta ce tana hada kai da sarakunan gargajiya na jihar domin tabbatar da dorewar zaman lafiya.
Gwamnan jihar Alhaji Abubakar Sani Bello ya shaida haka yayinda yake magana a gaban sarakunan da suka taru a fadarsa. Ya ce hankalinsa ya yi matukar tashi akan abun da ya faru a jihar Plato na kisan jama’a. Saboda haka akwai bukatar daukan matakin hana yaduwar al’amarin zuwa wasu wurare.
Yana cewa abubuwan dake faruwa a Jos ya dace a taimaka masu da addu’a, ko kirista kake ko musulmi kake, mutanen Jos na bukatan addu’a. An kashe mutanen da ba’a san iyakar su ba.
Gwamnan ya ci gaba da cewa muna zaune da shugaban kasa mutanen Miyetti Allah suka yi bayani, mutanen Berom suka yi bayani. Amma sai Allah ya ba gwamnan basira sai yaba dukkansu laifi. Amma abun da ya faru a Jos ina tabbatar maku ba maganar addini ba ne. Babu wani addini da zai ce ka samu mutum haka kawai ka kashe shi.
Shi ko shugaban majalisar sarakunan jihar Etsu Nupe Alhaji Yahaya Abubakar ya ce suna kokarin fadakar da jama’a mahimmancin zaman lafiya tare da kaucewa tsokanar juna musamman a wannan lokaci da hada hadar siyasa ke karatowa. Yace sukan fadawa mutane su ji tsoron Allah.
Yanzu da aka shiga cikin siyasa, ya kamata ayi taka tsan tsan waje manne manne da irin maganganun da ake yi. Ya ce suna jan hankalin jama’a suna yi masu gargadi kowa ya ji tsoron Allah su kiyaye dokokin kasa da dokokin siyasa.
Masana dai sun tabbatar da cewar sarakunan gargajiya da shugabannin addinai nada rawar takawa wajen dorewar zaman lafiya a tsakanin jama’a idan har gwamnati ta basu hadin kan da ya kamata.
A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Facebook Forum