Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miyetti Allah Ta Nisanta Kanta Da Cewa Rikicin Filato Daukar Fansa Ne


Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na kas, Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru
Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na kas, Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru

Kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a Najeriya ta nisanta kanta daga kalaman da wani ya yi da cewa kashe-kashen kwanannan a Filato ramuwar gayya ne Fulani suka yi.

Babbar kungiyar makiyaya ta Najeriya Miyetti Allah “CATTLE BREEDERS” ta nisanta kan ta daga labarin da ke cewa ta zayyana kashe-kashe a jihar Filato kwanannan da ramuwar gayya da makiyaya su ka yi don yadda a ka zalunce su a baya da sace mu su shanu.

Da ya ke magana a helkwatar kungiyar a Abuja, shugaban kungiyar na kasa Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru ya ce s,am kungiyar ba ta da alaka ta kusa ko nesa da wannan matsaya kuma sam kungiyar ba ta mara baya ga kashe mutane ba gaira ba dalili.

Ardon Zuru ya bukaci jami’an tsaro su zakulo duk wanda ya tada fitina su hukunta shi don kungiyar ba za ta taba mara baya ga zubar da jinin kowa ba,

"Ko ni ne na yi alifi zan ba da hadin kai don a yi mi ni hukunci" inji Ardon Zuru wanda ya bukaci gwamnati ta bincika don gano kungiyoyin Fulani na bogi.

Miyetti Allah wacce ta samu rijista da gwamnatin Najeriya fiye da shekaru 30, tana da hadin kai da sarakunan gargajiya inda Sarkin musulmi Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar ya ke matsayin shugaban kungiyar.

Saurari rohoton

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG