Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawarsu da shugaba Muhammadu Buhari, gwamnan jihar Filato Simon Lalong, ya bayyana cewa “rikicin ya yi sanadin rayukan mutane sama da 200” hukumomin sun bayyana rasuwar mutane 86 ne a ranar lahadin data gabata.
Rikicin da ya ki ci yaki cinyewa akan albarkatun kasa tsakanin manoma da makiyaya a yankin tsakiyar Najeriya, ya fi na ‘yan ta’addar Boko Haram muni wanda ya hallaka a kalla mutane dubu 20 cikin a kasa da shekaru 10.
Lamarin ya sa gwamatin shugaba Buhari, cikin binciken kwakwab yayin da ake kusa da sake zabe a shekara mai zuwa.
Shugaba Buhari ya dare karagar mulki ne a shekarar 2015, inda ya yi alkawari daidaita al’amura a kasar wadda tafi kowace yawan jama’a a Afirka.
Facebook Forum