Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Dr Bukola Saraki ya ce lokaci ya yi da ya kamata a za’a sake nazarin daukacin fasalin tsaro a Najeriya.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai ziyar jaje jihar Plato biyo bayan hare haren da suka lakume rayuka da dama a karshen makon jiya.
Dr Bukola Saraki wanda ya gana da gwamnan Plato Barrister Simon Lalong ya yi fatan Allah ya ba gwamnan basirar shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi jihar
Yace majalisa zata ci gaba da nazarin abubuwan da suke bukatan gyara domin a gyarasu. Ya ce dalili ke nan da suke duba wasu abubuwa da dama saboda matsalar tsaro da kasar ke fuskanta. Akwai matsala, kada mu dinga rudin kanmu. Kamata ya yi mu hada kai mu samo masalaha.
Shugaban majalisar dattawan ya bada tabbacin ci gaba da hada hannu da sauran sassan gwamnati domin tallafawa wadanda suka fada cikin wannan istilai inda ya kara da cewa majalisar zata yi duk abun da zata yi ta zakulo wadanda suke da hannu a cikin aika aikar da zummar hukunta su.
Shi ma tsohon shugaban kasar Najeriya Chief Olusegun Obasanjo ya kai ziyarar jaje jihar inda ya yi tur da hare haren. Chief Obasanjo ya ce ya fada kuma zai kara fada dole ne a gano musabbabin rikice rikicen.
Tsohon shugaban ya yi istifakin cewa dan Adam na da basirar warware kowace matsala.
A halinda ake ciki kuma kungiyar hadin kan kirista reshen arewacin Plato ta shirya zanga zangar lumana domin jawo hankalin gwamnati akan kashe kashen dake aukuwa a jihar. Reverend Nenman Gowon ya shaidawa Sashen Hausa cewa sun yi zanga zangar ce domin gwamnatin Plato tana daukan maganar tamkar wasa ne tare da cewa ‘yan siyasa ne suke haddasa rikicin. Amma abubuwan dake faruwa basu nuna hakan ba.
Amma zanga zangar ta rikide ta koma ta tashin hankali inda wasu masu zanga zangar suka farfasa motoci da tagan ofisoshin gwamnati.
Daraktan hulda da manema labarai na gwamnatin jihar Emmanuel Nanle ya fitar da wata sanarwa da ta nuna rashin jin dadin gwamnati akan lamarin . Sanarwar ta ce abun takaici ne a daidai lokacin da gwamnati ke kokarin samun daidaituwar lamura kungiyar zata bar wasu bata gari su shiga cikinta su lalata kayan gwamnati da motocin ma’aikata da baki a fadar gwamnati. Sanarwar ta ce gwamnati ta sha alwashin zakulo masu laifin. Kana daga bisani sanarwar ta yi kira ga ‘yan jihar su hada kai domin kawo karshen tashe tashen hankula dake yawan aukuwa a jihar.
A saurari rahoton Zainab Babaji da karin bayani
Facebook Forum