Kotu ta bayar da umurnin a ci gaba da tsare matashin nan dan shekara 19 da haihuwa, wanda ake tuhuma da laifin kashe-kashe na bayan nan cikin makarantu ko wuraren taruwar jama'a a Amurka.
Nikolas Cruz, wanda aka tuhuma da laifuffuka 17 na kisan kai, ya bayyana gaban wata kotu a Jihar Florida a cikin sarka, sanye da kaya launin ja irin na fursunoni. Lauyansa bai kalubalanci bukatar da masu gabatar da kara suka gabatar ta a ci gaba da tsare shi kafin a fara shari'arsa ba.
Cruz ya bayyana a gaban kotu 'yan sa'o'i a bayan da shugaba Donald Trump yayi gajeren jawabi kan wannan abin alhini a fadarsa ta White House inda yace yana jawabi ne ga kasa dake cikin zaman jimami.
Daga bisani a jiya alhamis, daruruwan mutane sun taru a bakin kofar makarantar sakandare ta Marjory Stoneman Douglas High School dake garin Parkland a Jihar Florida, domin jimamin mutanen da suka mutu.
An yi irin wannan zaman jimami a garuruwa masu yawa a fadin Amurka, ciki har da Jihohin California, Texas da Kentucky da manyan birane kamar Las Vegas.
Ana zargin Cruz da laifin bude wuta da wata babbar bindiga kan dalibai da malamai a wannan makarantar sakandare inda yake karatu kafin a kore shi a saboda rashin ladabi.
Babban jami'in tabbatar da bin doka da oda a karamar hukumar Broward inda wannan gari yake, yace Cruz ya bude wuta cikin ajujuwa 5 a hawa na daya da na biyu na ginin makarantar. A bayan da ya gama, Cruz ya jefar da bindigar da wata jakar dake bayansa cike da harsasai, ya kuma fita daga cikin ginin tare da sauran dalibai dake gudu.