Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakin Isira'ila da Siriya: Amurka Ta Ce Ta Na Tare Da Isira'ila


Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump.

Yayin da ake ta gumurzu tsakanin Isira'ila da Siriya mai samun goyon bayan Iran, Amurka, wadda ta sha nuna goyon baya ga Isira'ila, wannan karon ma ta fito ta bayyana goyon bayanta ga kasar ta bani-Yahudu a rigimarta da kasar Siriya mai samun goyon bayan Iran.

Wani bayani daga Sakataren Yada Labaran Fadar Shugaban Kasar Amurka ta White House ya kara jaddada cewa, “Kasar Isira’ila babbar aminiyar Amurka ce, kuma mu na goyon bayan amfani da damarta ta kare kanta daga Siriya mai samun goyon bayan Iran da kuma kungiyoyin ‘yan bindiga da ke kudancin Siriya.

Wannan bayanin ya biyo bayan harin da kasar Isira’ila ta kai jiya Asabar kan wasu muradun Iran da Siriya da dama a cikin kasar ta Siriya. Kasar Isira’ila ta kai hare-haren jiragen sama bayan da wani makamin harbor jirgin sama ya kakkabo jirgin yakinta yayin da yak e dawowa daga wani harin da ya kai kan wasu muradun Siriya da Iran ke tallafama wa a kasar ta Siriya. Kafin nan Isira’ila ta ce ta kakkabo wani jirgin Iran mara matuki wanda aka cillo daga Siriya bayan da ya shiga sararin saman Isira’ila da daren shekaran jiya Jumma’a.

A halin da ake ciki, a yau dinnan Lahadi, wani mai magana da yawun Sakatare-Janar na MDD ya ce duk wani mai ruwa da tsaki a Siriya da ma yankin baki daya, nauyi ya rataya a wuyanshi na kiyaye dokar kasa da kasa da kuma kudurorin Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG