Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbi Mutane Uku a Kusa Da Cibiyar Tsaron Amurka ta NSA


An harbi wasu mutane uku a yankin Fort Meade da ke jihar Maryland, inji hukumomin 'yan sandan yankin.

An harbe mutane uku a yau Laraba, a kusa da cibiyar tsaron kasar Amurka a wajen birnin Washington, a cewar rahotannin da ‘yan sanda suka bayar.

Kafafen yada labaran yankin sun ce an kama mutum daya, inda aka gan shi da ankwa a hannu ya na zaune a kasa yayin da ‘yan sanda suka kewaye shi a kusa da kofar shiga cibiyar ta leken asiri da ke unguwar da ake kira Fort Meade, a jihar Maryland.

A kusa kuma an ga wata bakar karamar mota da ta yi karo da wani shingen cibiyar.

Gilashin gaban motar ya yi kaca-kaca da harsashi kuma jakkunan kariya da ake kira “Air Bags” da turanci duk sun fito.

Ga kuma abubuwa da jini ya taba a kasa dab da inda abin ya faru.

Amma cibiyar da ake kira NSA a takaice, wadda ke aikin leken asiri ta na’urori a fadin duniya, da zummar dakile duk wata barazanar ta’addanci, ta ce ko mai na tafiya daidai a wurin.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG