A halin yanzu kum firayin ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, ya fada a jiya Litinin cewa ya tattauana da hukumomin Amurka akan yiyuwar Isra’ila ta kwace wasu yankunan Yahudawa dake bangaren Yammacin Kogin Jordan, amma a wani abinda ba’a saba gani ba, Amurka tace maganar tashi ba gaskiya bace, wanda yasa har aka ga kasashen biyu “a rana”, suna sabawa juna.
Yankunan da ake zance a kansu dai suna cikin wani yanki ne da Palesdinawa ke rike da shi, wanda suke son ya zama sashen kasarsu ta Palesdinu in ta sami ‘yancin kanta, amma kuma wanda Isra’ila ta mamaye a lokacin yakin da ta yi da kasashen Larabawa, wanda ake kira “Yakin Kwannaki Shidda” a shekarar 1967.
Kan haka ne, wani jami’I a fadar shugaban Amurka ta White House, Josh Raffel ya musanta kalamin na Netanyahu, inda yace karya ne, ba wanda ya tattauna wannan zance da gwamnatin Amurka.
Facebook Forum