Wani tsohon dalibin da aka kora a saboda rashin ladabi da biyayya ya bhude wuta a cikin wata makarantar sakandare dake jihar Florida da maraicen jiya laraba, ya kashe mutane akalla 17.
Babban jami'in kiyaye doka da oda na karamar hukumar Broward, Scott Israel, ya bayyana lamarin da cewa "rana ce mai alhini."
Yace wanda yayi harbin sunansa Nicholas Cruz, kuma 'yan sanda sun kama shi a wani wuri dake wajen makarantar ba tare da wata hayaniya ba.
Babban jami'in doka da odar yace an samu Cruz dauke da kwanson harsasai da dama, da kuma babbar bindiga guda daya.
Yace 12 daga cikin mutanen sun mutu a cikin makarantar, uku sun mutu a waje, yayin da guda biyu kuma suka mutu a asibiti a dalilin raunukan da suka samu. Wasu mutanen su akalla 14 sun ji rauni.
Yace wadanda abin ya shafa sun hada da dalibai da wasu mutanen manya, amma bai san ko malamai ne su ba.
Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Tarayya ta Amurka, FBI, ta tura jami'anta wadanda sune zasu jagoranci bincike ta hanyar yin aiki da 'yan sanda.
Makarantar sakandare ta Marjory Stoneman Douglas High School, tana garin Parkland, mai tazarar kilomita 72 a arewa da birnin Miami.
Hotunan telebijin da aka yi ta nunawa jim kadan bayan harbe-harben sun nuna dalibai suna kwararowa daga cikin makarantar, da yawa cikinsu sun daga hannu sama domin nuna cewa ba su dauke da makami.
Wannan lamari na jiya ya zo ma dalibai da hukumomin makarantar a ba-zata. Dalibai sun fadawa gidajen telebijin cewa komai na tafiya kamar yadda aka saba sai suka ji karar kararrawar da ake bugawa idan gobara ta tashi. Suka ce sun ji karar harbe-harben bindiga a lokacin da suke fita daga ginin makarantar, inda wasu suka koma ciki da gudu domin neman mafaka, wasu kuma suka tsere zuwa wani makeken kanti dake kusa da nan.
Hotunan bidiyo da aka dauka cikin makarantar sun nuna dalibai sun buya karkashin kujeru, inda aka ji wasu su na cewa sun ga harsashi ya huda fuskar wata kwamfuta.
Wasu sun buya cikin dakunan ajiye kayan sanyawa, suka yi ta aikewa da sakonnin Text na gaggawa ga iyayensu.
Facebook Forum