Kasuwar Kifi a Kusa da Baga ta Dawo

Wata mota da 'yan bindiga suka yi amfani da ita a garin Baga dake jihar Borno.

Daya daga cikin muhimman wuraren da tashin hankalin da jihar Borno ta samu kanta a ciki ya shafa, shine kasuwar kifi na kasa da kasa dake kan hanyar Baga, a cikin garin Maiduguri, inda wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su waye ba, suka abka wa kasuwar, suka kashe mutane da dama da lalata dukiya na miliyoyin Nairori.
Yanzu shekaru biyu kennan da kai wannan hari, ko wani irin hali kasuwar take ciki.

Mallam Mu’azu Isa Mado shine sakataren kungiyar masu kamun kifi da sayarwa. Yace “AlhamdulilLahi, yanzu zamu ce komai ya tafi lafiya, ba kamar baya ba. A yanzu mutane suna zuwa, suna saya kuma suna fita lafiya. Dama abunda muke bukata bako idan yazo, ya saya ya koma gida lafiya. To alhamdulilLahi, yanzu bamu da matsala. Bama gudu a kasuwa. Bawani abu haka zamu ci kasuwa lafiya mu tashi.”

Wakiliyar Muryar Amurka Sa’adatu Fawu ta tattauna da wasu ‘yan kasuwa kamar Abdullahi Alhaji Mudu Mai-kada “Gaskiya yanzu halin da muke ciki, bamu da matsala, muna cikin kwanciyar hankali. Muna gudanar da kasuwar mu, kamar yanda ya cancanta.”

A cewar kwararru akan harkokin tattalin arziki, kasuwar kifi na Baga shine babban kasuwar kifi a nahiyar Afirka.

Your browser doesn’t support HTML5

Kasuwar Kifi a Tashar Baga ta Dawo 2:10