Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zamu Sake Gina Gidajen Garin Baga - inji Gwamnatin Jihar Borno


Gwamnan Jihar Borno kennan a lokacin da yake kallon inda gidajen mutane suka kone a garin Baga dake arewacin wannan jiha.
Gwamnan Jihar Borno kennan a lokacin da yake kallon inda gidajen mutane suka kone a garin Baga dake arewacin wannan jiha.

Gwamnatin Jihar Borno ta ce zata sake gina gidajen da aka kona a garin Baga a lokacin fadan da aka yi a karshen mako.

WASHINGTON, D.C - An kashe mutane da dama a lokacin wani kazamin fadan da aka gwabza tsakanin masu kishin Islama da dakarun tsaron gwamnatin Najeriya a yankin arewacin kasar.

Kungiyar agajin Red Cross ta Najeriya ta fada yau litinin cewa mutane akalla 187 ne suka mutu a wannan fadan, yayin da ake jinya ma wasu su 77.

Amma kuma, wani kakakin rundunar sojoji a Jihar Borno yace an yi karin gishiri a rahotannin yawan wadanda suka mutu din.

Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Alfa Ahmed ya tattauna da mai baiwa Gwamna kashin Shettima shawara kan hulda da jama’a, Isah Umar Gusau, ko mene ne dalilan yin hakan?

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

An fara gwabza wannan fada ranar jumma’a da daddare a garin Baga dake bakin tabkin Chadi, abinda ya tilasta ma dubban wannan gari da ya shahara wajen kamun kifi tserewa cikin jeji.

Mutanen garin na Baga sun ce an goce da fada a lokacin da sojoji suka kewaye wani masallacin da aka yi zargin cewa ‘yan kungiyar nan ta Boko Haram sun buya a ciki.

An yi musanyar wuta sosai, inda aka ce ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun yi amfani da muggan makamai ciki har da gurnetin da ake cillawa da roka. Sojoji da kuma jami’an yankin sun ce ‘yan kungiyar sun yi amfani da fararen hula a matsayin garkuwa, yayin da mazauna garin suka ce da gangan sojoji suka yi ta cinna wuta a gine-gine lokacin wannan harin.

Wani kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Patrick Ventrell, ya fada yau litinin cewa Amurka tana goyon bayan kokarin gwamnatin Najeriya na hukumta masu zub da jini, amma kuma yace tilas ne ta mutunta hakkin jama’a, kuma tilas ta takali koke-koken mutanen arewacin Najeriya.

Yace, "Martaninmu shi ne ba matakan tsaro ne kawai zasu iya murkushe tsageranci ba. Kungiyar Boko Haram tana fakewa da koke-koken zahiri na mutanen arewacin Najeriya wajen neman magoya baya tare da samun tausayawar jama’a. Saboda haka abinda za a yi shi ne a takali wasu daga cikin bukatu da kuma damuwa na zahiri na al’ummar arewacin Najeriya ta yadda kungiyar ba zata iya fakewa da su ba."
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG