WASHINGTON, DC —
Kakakin rundunar tsaron hadin guiwa ta kasa da kasa dake bakin iyakar Najeriya da Chadi da Kamaru da kuma Jamhuriyar Nijar, ya bayyana cewa babu abinda masu son tayar da fitina ke juyawa domin cimma muradunsu, kamar irin fitinar da ta faru a garin Baga, inda ake ta yada labarai marasa tushe ko hujja kan adadin mutanen da suka mutu.
Kanar Sagir Musa, yace adadin mutanen da suka mutu a fitinar ta Baga, ya saba sosai da ainihin abinda ya wakana, yana mai bayyana cewa idan akwai wanda ya san inda kaburburan daruruwan mutanen da aka kashe suke, to ya zo ya nuna musu ko ya nuna ma duniya.
Kanar Sagir Musa, ya kuma yi bayani dalla-dalla na abubuwan da suka faru, da kuma lokutan da suka faru din: