Da yake zantawa da 'yan jarida a Maiduguri, bayan wata ziyarar gani da ido da ya kai zuwa garin Baga, sanatan yace ya tarar da mutane cikin mummunan hali na jinkai, inda yace tantuna guda biyu kadai na hukumar agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA, ya gani a wurin, kuma mutane su na kwana tare da wuni a filin Allah saboda sun rasa matsuguni,
Ya kuma ce gidaje akalla dubu 4 ne aka kona su kurmus a wannan gari da ya shahara wajen kamun kifi a bakin iyakar Najeriya da Chadi.
Wannan adadi na sanatan, ya sha bambam da mutane 36 da hukumomin sojan Najeriya suka ce an kashe, da kuma 187 da kafofin labarai suke ambata daga bakin wani jami'in gwamnatin jihar Borno.
Ga rahoton wakilinmu Haruna Dauda Biu daga Maiduguri.