Kasar China Na Taimakawa Najeriya Wajen Gina Tashar Wutar Lantarki

Wutar lantarki, Najeriya

Kamfanin makamashi na “Mainstream” a Najeriya, wanda tuni yake gudanar da manyan tashoshin samar da wutar lantarki guda biyu a kasar, ya fara gudanar da wani sabon ginin da kasar China ta samar, kusan shekara guda bayan samun wannan damar in ji kamfanin a jiya.

WASHINGTON, D. C. - Kamfanin makamashin “Mainstream Energy Solution Ltd” ya ce reshensa na Penstock Energy Ltd yana gudanar da sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 700 a garin Zungeru dake tsakiyar Najeriya, wanda aka gina da lamunin dalar Amurka biliyan 1.3 daga kasar China.

Hukumar kula da kamfanonin gwamnati ta Najeriya, BPE, a watan Fabrairun da ya gabata, ta ba da rangwamen ga Mainstream Energy, wanda zai biya gwamnatin Najeriya dalar Amurka miliyan saba’in (70) daga nan har zuwa sama da shekaru 30 don ci gaba da ayyukan kamfanin.

A cikin shekaru goman da suka gabata, kasar China ta taka rawar gani a Najeriya, inda ta samar da kudi ta bankin raya kasa don gina ababen more rayuwa da suka hada da layin dogo, filayen jiragen sama, da tashoshin samar da wutar lantarki.

Kamfanin samar da wutar lantarki na Kainji da Jebba da ke karkashin Mainstream Energy sun hada da megawatt 1338 wanda ya kai kusan kashi 33 cikin 100 na wutar lantarkin da Najeriya ke samarwa a halin yanzu mai karfin megawatt 4000.

Akwai bukatar kari da yawa yayin da miliyoyin gidaje da wuraren kasuwancin ke ci gaba da fama da rashin wuta akai-akai.