Rashin Ingantacciyar wutar lantarki a Najeriya na daga cikin matsalolin da ke ci wa al'ummar kasar tuwo a kwarya, a shekarar da ta gabata an samu katsewar wutar lantarki har sau 12 a kasar.
Matsalar wutar lantarki a Najeriya, wani abu ne da ‘ƴan kasar ke fatan ganin an kawo karshensa.
A jawabinsa na sabuwar shekara, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya sha alwashin magance matsalar wutar lantarki a kasar cikin watannin 24.
Tinubu ya ce za su yi iya kokarinsu domin ganin an hanzarta inganta wutar lantarkin da kowanne dan kasa zai mora.
Idan za'a iya tunawa, a taron COP28 da ya gudana a Hadaddiyar Daular Larabawa a watan Disambar shekarar da ta gabata, Najeriya da kasar Jamus sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar inganta wutar lantarki a Najeriya, wanda kamfanin Seimens na kasar Jamus zai gudanar da aikin gyara matsalar ta wutar lantarki a kasar.
Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, a lokacin mulkinsa ya taba bai wa kamfanin na Seimens kwangilar dalar Amurka biliyan Shashida ($16B), domin inganta harkar wutar lantarki a kasar, wanda har izuwa yanzu ba ta gyaru ba.
Wasu sun ‘yan Najeriya sun ce wannan ne karo na uku da ake bai wa kamfanin Siemens kwangilar gyara harkar wutar lantaki a kasar, kuma suna fatan wannan karon ya zama an yi nasarar gyaran.
A hirarsa da Muryar Amurka, Rilwan Ladan, manazarci kuma mai sharhi akan al'amuran yau-da-kullum ya ce, "bawa kamfanin Seimens abu ne me kyau, kuma idan har ana so a magance matsalar wutar lantarki a kasar, sai Shugaba Tinubu ya yi tsayin daka tukunna, idan kuma ba haka ba, tarihi ne zai maimaita kansa.
Yanzun dai 'yan Najeriya na dakon ganin yadda gyaran wutar lantarkin zai kasance nan da watanni 24 kamar yadda Shugaba Tinubu ya sha alwashi.
Saurari cikakken rahoton Rukaiya Basha:
Dandalin Mu Tattauna