Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ayyukan Masana’antu A Kano Sun Tsaya Cik Sanadiyyar Katsewar Wutar Lantarki


lantarki
lantarki

Rahotanni daga Kano a Najeriya sun ce ayyukan manya da kananan masana’antu a birnin sun tsaya cik sanadiyyar katsewar wutar lantarki da aka fuskanta tsawon sa’o’i da dama a sassan kasar, al’amarin da ya haifar da mummunan koma baya ta fuskar hadahadar tattalin arziki.

Yankunan birane da na karkara a fadin Najeriya sun kasance cikin mummunan yanayin halin duhu saboda daukewar hasken lantarki, sanadiyyar durkushewar na’urorin da ke samar da wuta daga cibiyoyin sarrafa lantarki na kasar.

Kodayake, dama ‘yan kasar na kokawa da kamfar lantarki tsawon shekaru masu yawa, amma ga alama yanayi na wannan karon ya jefa al’umma cikin mawuyacin hali.

Wani magidanci mai suna Malam Tajudeen ya ce sun kwashe fiye da makonni biyu ba su da hasken lantarki a Unguwarsu, tun gabanin durkushewar na’urorin lantarkin na Najeriya.

“Sai a kawo ta ba za ta wuce dakikoki biyar ba an dauke ta, sai dai mutum idan yana da kudi ya sayi mai ya zuba a injinsa na gida domin ya ga haske, wasu kuma masu sukuni su saka na’urar lantarki mai amfani da hasken rana." Tajudeen ya ce.

Ya kara da cewa, "ga wannan tsananin zafe da ake fama da shi a gari, ga mai ya yi tsada, lita daya sama da naira dari 600, duka biyu fa kenan ga ba abinci ga ba wuta, to da wanne mutum zai ji? a cewar sa.”

Ga alama wannan yanayi ya durkusar da aikace-aikacen manyan kamfanoni, kanana da matsakaitan masa’antu a birni da kewayen Kano.

Alhaji Sulaiman Abubakar na daya daga cikin mamallaka kamfani a rukunin kananan masana’antu na Dakata a Kano.

"Ba za mu iya fadar yawan asarar da muka yi ba, gaskiya abu ne mai wahala.”

Kimanin shekaru 10 da uska shude ne, gwamnatin Najeriya ta sake fasalin samar da wuta a kasar, inda kamfanoni dake samarwa da kuma rarraba lantarkin kowa ke cin gashin kansa.

Kamfanin KEDCO shike rarraba hasken lantarkin a jihohin Kano Jigawa da kuma Katsina, kuma Sani Bala Sani shine kakakin kamfanin mai shalkwata a Kano. “Kai tsaye ba mune da alhakin gyaran wadannan na’urori da suka durkushe ba, ‘yan uwan mu ne Kamfanin TCN dake samar da hasken lantarki a kasa baki daya.”

Ana daf da kammala wannan rahoto ne, rahotanni suka bayyana cewa, kamfanin TCN ya samu nasarar dawo da hasken lantarkin a wasu sassan kasar bayan farfado da ayyukan na’urori a cibiyar bada wutar lantarki ta kasa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG