SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da shugabannin majalisar dokoki ta Jihar Kebbi suka ce sun sauka daga mukamansu, kuma majalisar ta nemi gwamna ya bayyana a gabanta.
Duk da yake manyan jam'iyun siyasa a Najeriya sun himmantu wajen neman nasarar zabe, wasu suna ci gaba da zama dabaibaice da matsalolin cikin gida, kamar yadda jam'iyar adawa ta PDP ta kasa shiryawa da gwamnonin ta da ke yi mata barazana, ita kuwa jam'iyar APC mai mulki kwananan aka ji dan takarar ta na kokawa akan matsalolin da kasa take ciki a haujin karamcin mai da canjin kudi da yake gani na iya kawo masa matsala.
A Jihohi ma ana samun irin wannan takin saka a jam'iyun kamar yadda yake faruwa yanzu a jihar kebbi dake arewa maso yammacin Najeriya inda ‘yan majalisar dokokin jihar ke kai ruwa rana da gwamnan jihar Sanata Abubakar Atiku Bagudu.
Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar ya ce dukan masu rike da mukamai sun yanke shawarar jingine mukaman nasu kuma ‘yan majalisa ashirin sun aminta da kudurin yin hakan.
Wata takarda da majalisar ta fitar ta baiwa gwamnan umurnin ya bayyana a gaban ta domin warware wata takaddama ta wasu kudade da ta amince masa ciyo bashi.
Sai dai wasu manyan jami'an gwamnatin Jihar ta kebbi sun dira cikin majalisar suka zauna da ‘yan majalisar a kokarin warware takun sakar inda aka dauki dogon lokaci ana tayar da jiyoyin wuya.
A karshe duk kokarin da manema labarai suka yi domin jin sakamakon zaman ya faskara.
Masu rajin bunkasa tsarin dimokradiya a Najeriya irin Malam Shehu S. Kudu na ganin cewa idan an dafa boye ba'a ci boye shine ke sa irin wadannan matsalolin na fitowa fili.
Muryar Amurka ta tuntubi kakakin jam'iyar APC a Jihar Kebbi Isa Assalafi akan irin yadda wasu ke ganin rashin mutuwar bata rasa nasaba da batun kudi sai dai ya ce rikici tsakanin ‘yan siyasa da ma shi ne sha'awar tsarin dimokradiya.
Mun yi kokarin ji daga ko da daya daga cikin ‘yan majalisar akan yadda jama'a ke ganin ruwa ne ke son karewa dan kada bai gama wanka ba, sai abin ya ci tura.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Your browser doesn’t support HTML5