Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben 2023: Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawal Ya Amince Da Hukuncin Kotu


Shugaban Majalisar Dattawa na 9, Ahmad Ibrahim Lawal
Shugaban Majalisar Dattawa na 9, Ahmad Ibrahim Lawal

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmad Lawal ya amince da Bashir Machina a matsayin dan takarar jam’iyyar APC a zaben Sanatan Yobe ta Arewa a shekarar 2023.

WASHINGTON, DC - A wata sanarwa da ya fidda a shafinsa na twitter, Lawal ya ce bayan tattaunawa da ‘yan siyasa abokan huldarsa da magoya bayansa ya yanke shawarar ba zai daukaka kara ba, ya amince da hukuncin kotun.

Bayan haka ya gode wa Sanata Ibrahim Gaidam na jam’iyyar APC da gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, da kuma ‘yan mazabarsa saboda goyon bayan da suka bashi.

A ranar Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke Yobe ta umurci hukumar zabe ta INEC da ta amince da Machina a matsayin dan takarar kujerar dan majalisar dattawa, bayan da Lawal da Machina suka kwashe watanni suna sa-in-sa akan neman kujerar.

Tun a shekarar 1999 aka fara zaben Lawal a majalisar wakilai, kafin daga baya aka zabe shi a majalisar dattawa, sannan a shekarar 2019 ya zama shugaban majalisar dattawan kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG