Wannan na zuwa ne yayin da ya rage kasa da kwanaki 30 a gudanar da zaben shugaban kasa da ake sa ran ‘yan Najeriya sama da miliyan 93 za su fita domin kada kuri’a.
Batun wayar da kan al’umma dai na ci gaba da daukar hankali ne musamman a daidai lokacin da wasu masu sharhi a kan al’amurran siyasa daban-daban ke gudanar da tarukan muhawara, don yin nazari a kan manufofin da manyan ‘yan takara kamar PDP, APC, LP da NNPP suka gabatar, don ya zama wani mataki na sanya ido a kan duk wanda Allah ya bawa nasara a zaben na watan Fabrairu, ya cika duk alkawurran daya dauka ko a nemi yadda za’a tsige shi daga kan karagar mulki.
Duk da cewa akwai banbanci a manufofin ‘yan takarar shugaban kasa daban-daban da ma yanayin da suka ce zasu aiwatar da su, ‘yan Najeriya na dada bayyana muhimman abubuwa da ya kamata duk wanda ya sami nasara ya mayar da hankali a kai, kamar farfado da komadar tattalin arziki, samar da hanyoyin ba wa matasa ayyukan yi da koya musu sana’o’i, yaki da matsalolin tsaro kai tsaye ba kakkautawa, farfado da matattun masana’antun kasa, inganta bangaren ilimi da dai sauran su, suna cewa a wannan karon zasu sanya ido a kan duk wanda ya sami nasara don ya cika alkawurra daya dauka.
Haka kuma, ‘yan takarar LP, APC, da PDP duk sun amince da irin barazanar da ake fuskanta a kasar tare da bayar da shawarwari daban-daban da suka hada da sake fasalin yadda aikin 'yan sanda ke tafiya, inganta ayyukan tsaro, inganta tsarin makamai, zamantakewar jama'a da karfafa tattalin arziki.
A hirarshi da Muryar Amurka, Kwamared Salihu Dantata Mahmud, mai sharhi a kan al’amurran siyasa, ya ce ya yi marhaba da batun wayar da kan al’umma a game da manufofin ‘yan takarar shugaban kasa daban-daban, don su iya bibiya idan aka rantsar da sabon shugaban kasa, yana mai cewa an dade ana yin hakan a kasashen da aka ci gaba ba wai kawai a filin gangamin yakin neman zabe ne ‘yan takara ke bayyana manufofinsu ba.
A wani bangare kuma, Khadija Suleiman Aliyu, ambassada a ayyukan wayar da kan ‘yan kasa a game da manufofin ‘yan takara, ta ce kamata ya yi duk wanda ya sami nasara a zaben watan Febrairu ya mayar da hankali a kan matsalar tsaro, da magance matsalar tsadar kayayyakin masarufi.
Ita ma da take yin tsokaci, Hajiya Suwaiba Shehu Ibrahim, malama a jami’ar gwamnati jihar Kaduna, ta bayyana cewa dole ne a kara yin hobbasa wajen ilimantar da ‘yan kasa a game da manufofin ‘yan takara, saboda a fahimci menene wadannan manufofi, ya suka shafi rayuwar al’umma ta yau da kullum, da kuma yadda suka banbanta da manufofi ko alkawurran wasu ‘yan takara a baya, domin a iya sanya ido a kan duk wanda ya sami nasara a zaben mai gabatowa.
Tuni dai wasu masu ruwa da tsaki ke dasa alamar tambaya a kan yiyuwar aiwatar da dukkan manufofin manyan ‘yan takara da shirye-shiryen da suke kan yi don cimma wadannan manufofi.
A wannan zaben dai, hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ce an sami karin ‘yan Najeriya miliyan 9.3 da zasu iya jefa kuri’a a wannan zabe mai zuwa, kuma masu sharhi na ganin cewa zabi ya koma kan masu kada kuri’a a kan yadda zasu fuskanci alkawuran da ‘yan takarar suka dauka a fannin kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki, yaki da matsalolin tsaro, farfado da komadar tattalin arziki da dai sauransu ga duk wanda ya sami nasara.
Wasu masu sharhi na ganin cewa manufofin da manyan ‘yan takarar suka gabatar basu wadatu ba musamman a kan tsaro, kuma dole ne duk wanda ya sami nasara ya dauki matakan gaggawar sake duba alkawuran yakin neman zabensa tare da ba da fifiko ga cikkaken garambawul da zai tabbatar da tsaro a Najeriya.
Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf: