Akwai ra'ayin dake cewa a tsaya har sai wata shida nan gaba lokacin da za'a sabunta dokar ta baci a ga abun da zai faru.
Janar Saleh Maina mai ritaya shi ya yi garkuwa da marigayi Muhammad Yusuf a shekarar 2009 mutumin da ya kafa kungiyar Boko Haram. Daga baya ya mika shi Muhammad Yusuf ga 'yansanda a Maiduguri.
Janar Maina yace an yi kurakurai da yawa. Inji shi ba kowace fitina ba ce ake tunkara da yaki. Ba koyaushe ake anfani da karfin soja ba. Yace akwai fitinar da idan ta taso sai a zauna a tattauna. Yace tana yiwuwa yanzun ma ana shirin tattaunawa da 'yan ta'adan. Tana yiwuwa kuma ana shirin wani sabon damarar yakansu ne.
Janar Maina yace an bari ne abubuwa suka lalace shekara da shekaru. Yace ya sani Ingila da Arewacin Island sun yi shekaru fiye da talatin da biyar ana ta'adanci. A kasar Sri Lanka ma hakan ya faru. Yanzu rikicin kasar Najeriya bai wuce shekaru hudu ba kodayake ba'a fatan ya cigaba.
Idan ba'a samu shugaban da ya mayarda hankali ba za'a dade ana zubar da jini da asarar dukiyoyi. Yana fatan shugaba Buhari da gaske ya keyi ya kawo karshen ta'adanci a kasar.
Jam'iyyar APC da mukarraban gwamnatin Buhari na cewa nuna hakuri kadan zai bada daman ganin sauye sauye masu tasiri. Sakataren APC na kasa Maimala Boni. Yace kasar kusan a durkushe take. Da nan da nan akwai shinge kuma kowa ya san abubuwan dake faruwa a shingayen. Amma yau babu su. Yace nan ba da dadewa ba komi zai daidaita a karkashin shugabancin shugaba Buhari.
Yace Najeriya zata samu zaman lafiya. Mutuncin kasa zai dawo a cikin kasashen duniya. A cikin gida ma 'yan kasa zasu ga kiman shugabanni da jami'an tsaro domin tabarbarewa alamura sun sa mutanen Najeriya basa ganin mutuncin jam'an tsaro.
Ga rahoton Nasiru El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5