Kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta yi dirar mikiya kan gwamnatin Tinubu bayan karin farashin fetur daga Naira 617 zuwa Naira 897 a farashin hukuma.
NLC ta ce wannan tamkar cin amanar yarjejeniyar karin mafi karancin albashi ne zuwa Naira 70,000.
An wayi gari a ranar Talata gidajen man da ke karkashin kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL sun kara farashi da fiye da N250 in a ka yi la’akari da yandda a ka sayar da man a gidaje daban-daban.
Ma’abota motoci sun yi cirko-cirko ko su bi dogon layi su sha a farashin gwamnati ko kuma su saya a bakar kasuwa da dan karen tsada daga Naira 1400-1500.
NLC a sanarwa ta ce ta amince da karin Naira 70,000 a mafi karancin albashi da alkawarin ba karin farashi don gwamnatin ta ce in ta kara albashin mafi karanci zuwa Naira 250,000 to lita za ta koma Naira 1500-2000.
NLC ta ce ba za ta lamunci barazana ba kuma ta na kira a dawo da farashin yanda ya ke gabanin yarjejeniyar.
Komred Nasiru Kabir jami’in kungiyar kwadagon ne “ba za mu daina tsayin daka kan mafi karancin albashi ba kuma ba za mu bari a ci zarafin shugabannin kungiyar mu ba don a na yin hakan ne don rufe bakin mu”
NLC ta ce har zuwa yanzu ba a fara biyan mafi karancin albashin ba na N70,000 wanda dama bai isa ba sai ga sabuwar magana.
Gwamnatin Bola Tinubu na nanata cewa harkar fetur ta zama kasuwa ne ke yin halin ta don ba batun tallafi duk da a na radeardin ba da tallafin.
Kazalika ta musanta ba kamfanin na NNPC umarnin ya kara farashin na litar mai.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Ministan Mai, Sanata Heineken Lokpobiri ya nesanta gwamnatin da ba da umarnin karin “kamar yadda ake yadawa a kafafen sada zumunta.”
“Muna masu Allah wadai da wannan ikirari da ba shi da tushe, wanda yunkuri ne na fusata jama’a.” Sanawar ta ce.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El Hikaya:
Your browser doesn’t support HTML5